June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikicin Libya Ya Shiga Wani Sabon Yanayi – Guterres

1 min read

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa”lokaci na kurewa” a Libya, yana mai cewa rikicin da ake yi a kasar ya shiga wani sabon yanayi, yayin da katsalanda daga kasashen waje ta kai wani mataki da ba a taba gani ba.

“Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da aiki tare da bangarorin da ke fada don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma komawa hanyar siyasa don samar da maslaha,” abinda Antonio Guterres ya fada kenan a wani muhimmin taro ta yanar gizo da ya yi da kwamitin sulhun Majalisar Dikin Duniya.

Ya ce katsalandan kasashen na ketare ya hada da kai miyagun makamai da mayaka kasar, abubuwa biyu da suka saba wa takunkumin makaman da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wa Libya.

A cikin makonnin baya-bayan nan, dakarun bangaren gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya da ake kira GNA a takaice, sun sami nasara akan mayakan kwamanda Khalifa Haftar na dakarun LNA da suka kwashe tsawon watanni 14 suna kai farmaki kan Tripoli babban birnin kasar.

Dakarun GNA kuma sun kwace ikon wani filin jirgin sama da wasu muhimman garuruwa biyu a arewa maso yammacin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *