June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Amurkawa na yi China kallon abokiyar gaba – China

1 min read

Ministan harkokin wajen China Wang Yi, ya ce akwai wasu jama’a a Amurka ke wa Chinar kallon babbar abokiyar gaba.

Ya ce kasashen biyu ba su taba fuskantar tsamin dangantaka ba kamar a wannan karon.

Gwamnatin Shugaba Trump na matsa wa China lamba kan harkokin kasuwanci da tauya hakkin bil’adama da kuma annobar Korona.

Mr Wang ya bayyana cewa Amurka na wa shirye-shiryen Chana mummunar fahimta, amma yana da tabbacin cewa za su dinke barakarar da ke tsakaninsu.

Amurka na yi wa Chana kallon marar gaskiya, shi yasa duk wani abu da ya shafi gwamnatin China take ganin babu gaskiya a ciki, kuma ba ta da hujja kan hakan.’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *