June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Bindiga sun kai hari kauyukan Gabashin Jihar Sokoto.

2 min read

Yayin da rundunar sojan saman Najeriya ta kaddamar da wasu hare-hare akan ‘yan bindigar da ke dazuzzukan gabashin jihar Sokoto, ‘yan bindigar sun maida martani kan jama’ar kauyukan karamar hukumar Isa lamarin da wasu ke gani wani koma baya ne ga nasarar da sojojin saman Najeriya suka samu.

Shugaban Rundunar Adalci a jihar Sokoto, Bashir Altine Guyawa, ya ce akwai bukatar daukar mataki na bai daya tsakanin sojan sama da kasa a lokacin kai hare-hare a kan ‘yan bindigar.

Bashir ya kuma kara da cewa yanzu haka ‘yan bindigar sun tarwatsa kauyuka talatin da daya, yayin da jama’a ke yin hijira zuwa garuruwan Isa da Shinkafi ta jihar Zamfara.

Shugaban Sojan Saman Najeriya, Sadiq Abubakar, ya ce suna aiki kafada da kafada da takwarorinsu da ke kasa wajan yakar ‘yan bindigar a gabashin jihar Sokoto, inda suke lugudan wuta ta sama su kuma sojojin kasa suna tisawa.

Wasu jama’ar yankin gabashin jihar Sokoto da suka nemi a sakaya sunayensu sun ce ‘yan bindigar suna shigowa su kwace kayayyakin jama’a su kuma kashe su.

“Bayan daukar matakin bai daya akwai bukatar gwamnati da masu hannu da shuni su kawo dauki ga ‘yan gudun hijira da suka baro kauyukansu zuwa garin Isa sanadiyar hare-haren,” a cewar dan majalisar dokoki na jiha mai wakiltar karamar hukumar Isa, Habibu Halilu modaci.

Duk da girke sojojin kasa a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni, a kwanakin baya gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya sheda wa al’ummar yankin cewa ma’aikatar ‘yan sandan Najeriya za ta kafa rundunar ‘yan sandan ko-ta-kwana a yankin duka, domin samar da tsaro.

Yanzu dai an zuba ido a ga irin matakan da rundunar sojojin za ta dauka a kan ‘yan bindigar game da sabbin hare-haren da suka kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *