Yanzu-Yanzu An kama mutum 4 da zargin ‘lalata’ yara.
1 min read
Hukumar tsaron al’umma a Najeriya ta Nigeria security and Civil Defence Corps wato NSCDC, ta yi nasarar cafke wasu mutum huɗu tare da gurfanar da su a gaban kotu, waɗanda ake zargi da lalalata ƙananan yara.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai ɗan shekara 35 wanda ake zargi da lalata yarinya ‘yar shekara shida, sai kuma wani ɗan shekara 30 wanda ake zargi da lalata ‘yar sjekara shida, inji wani babban kwamanda a hukumar Muhammad Gidado.
Ya kuma bayyana cewa akwai wani ɗan shekara 39 da aka kama wanda ake zargi da lalata yarinya ‘yar shekara bakwai sa’annan kuma akwai wani ɗan shekara 41 wanda ake zarginsa da lalata wani yaro ɗan shekara 10.
Article share tools