July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu-Yanzu ‘Yan sandan Najeriya sun kama gungun ‘yan fashi.

2 min read

Jami’an ‘yan sanda na runduna ta musamman a Najeriya sun kama gungun ‘yan fashi na mutum bakwai da suka kai hari tare da yin fashi a wasu bankuna uku da ke jihohin Ondo da Ekiti a kudu maso yammacin Najeriya a tsakanin shekarun 2019 da 2020.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda kasar ta aike wa manema labarai a ranar Alhamis, inda ta ce a yayin ta’addancin ‘yan fashin sun kashe mutum shida da suka hada da ‘yan sanda tare da sace miliyoyin naira.

Bincike ya nuna cewa ‘yan fashin masu tsakanin shekaru 36 zuwa 50, sun yi fashin ne a wani bankin kasuwanci da ke Ile-oluji, a jihar Ondo ranar 7 ga watan Fabrairun 2020, inda aka kashe ‘yan sanda hudu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen na da hannu a fashin da aka yi a wani bankin ba da rance da ke Idanre, a jihar Ondo a watan Disamban 2019 da kuma wani bankin kasuwanci da ke Oye Ekitia jihar Ekiti, inda ‘yan sanda biyu suka rasa rayukansu.

Rundunar ta ce ana ci gaba da kokarin kama sauran mutanen da ke cikin gungun don kwato muggan makamai da suke amfani da su.

A wani lamarin mai kama da haka kuma, rundunar ta ce an kama wasu mutum 23 masu hannu a laifuka kamar satar mutane don kudin fansa da fashi da mallakar muggan makamai.

”Nan gaba kadan za a gurfanar da mutanen a kotu bayan an kammala bincike,” a cewar sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *