An hana ƴan Najeriya neman aiki a Dubai
1 min read
Ƴan Najeriya na bayyana fushinsu a shafukan sada zumunta bayan da aka wallafa wani tallan neman ma’aikata a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda a ciki aka fito karara ana cewa ba a bukatar ƴan Najeriya su nemi aikin.
Tallan da kamfanin Shirley Recruitment Consultants ya wallafa a shafinsa na intanet ya sanar da masu neman aiki cewa ana neman wadanda za su iya aikin tallan turare ne a Dubai, kuma ana bukatar su kasance masu kwarewa kan harkar kasuwanci na a kalla shekara uku.
Tallan ya kuma ce “ƴan Afirka maza ko mata na iya neman aikin amma ban da ƴan Najeriya.”