Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020
1 min read
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudin kasar na 2020.
A kasafin kudin, wanda majalisun dokokin kasar suka yi wa kwaskwarima a watan jiya, za a kashe N10.8 a shekarar ta 2020.
Mai taimaka washugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a.
Sai dai bai yi cikakken bayni kan kasafin kudin ba.