June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Neja-Delta ta bayyana yadda ta raba wa ma’aikatanta N1.5bn na tallafin korona

2 min read

Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta bayyana wa wani kwamitin majalisar dattawan Najeriya da ke binciken ta dalilan da suka sa ta raba wa manyan shugabanni da ma’aikatan hukumar ta NDDC naira biliyan 1.5. Yayin wani zama da aka yi a majalisar kasa da ke Abuja, shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya bayyana yadda aka raba kudaden:Shugaban riko na hukumar NDDC Kemebradikumo Pondei ya bayyana cewa:

“Tun farko shigowar Covid-19 muka dauki matakin bayar da tallafi ganin cewa aikin NDDC ne ta bayar da tallafi”.

Ya kuma ce, “muna da kalubalen da suka sa muka bayar da tallafin naira miliyan 775 ga jihohi tara.”v”Kuma bayan wannan akwai wasu naira miliyan 170 na daban. Muna da mazabun sanatoci 27 a NDDC kuma saboda matsin da muke samu daga masu ruwa da tsaki a yankinmu, sai muka kasafta kuma muka sami amincewar rabawa kungiyoyin matasa kana muka ba kungiyoyin mata naira miliyan biyar su ma.

“Akwai kuma masu naƙasa a kowace mazabar sanata daga jihohi tara da kudinsu ya kai naira miliyan 270, kamar yadda ya fada.”

Game da ma’aikatan hukumar, ya ce: “NDDC na da ma’aikata fiye da 4,000 a jihohi tara na kudancin kasar nan, kuma kowannensu tamkar wakilcin jama’arsa yake. Mun fuskanci matsi sosai kan batun, shi ya sa muka biya kudaden.

“Mun yi haka ne domin rage tasirin annobar kan matasa tun da ba sa aikin komai. Mun bayar da tallafin ne domin kauce wa tashin hankali,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *