April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Makomar Almajiranci a Kano

2 min read

Hukumar kula da makarantun Al-Qur,ani da Islamiyya ta jihar Kano ta karbi rahoton Kwamitin da Dandalin mahaddata Al-Qur,ani da Alarammomi na duniya reshen jihar Kano suka kafa domin baiwa Gwamnati shawara kan yadda zaa fasalin makarantun Tsangayu da na Allo a jihar Kano.
Shugaban Hukumar Sheikh Gwani Yahuza Gwani Danzarga ne ya karbi rahotan lokacin da Yan Kwamitin suka Kawo masa ziyara a ofishinsa inda yace Gwamnatin jihar Kano tana cigaba da gudanar da sababbin tsare-tsaren bunkasa makarantun Tsangayu da na Allo domin kyautata karatun Al-Qur,ani a jihar Kano.
Gwani Yahuza Gwani Danzarga ya kara da cewa tuni hukumar sa tare da Gwamnatin jiha suka dukufa wajen aiwatar da kyakkyawan tsari run kafin kafa wannan Kwamiti.
A jawabinsa tun da farko shugaban Kwamitin wanda kuma Malami ne a Jami,ar Yusuf Maitama Sule Gwani Dr. Ibrahim Ilyasu Adam yace akwai bukatar Gwamnati ta kara Samar da makarantun Tsangayu guda dai dai a kananan hukumomi 44 Na jihar Kano domin kyautata karatun Al-Qur,ani a jihar Kano.
Dr. Ibrahim Ilyasu yace kamata yayi Gwamnati ta yi doka ta musamma wacce zata tilastawa iyayen yara daukar nauyin karatun yayansu a makarantun Tsangaya da na Allo a ko,ina sannan ta hada kai da kungiyoyi masu zaman Kansu da Attajirai da dukkanin masu ruwa da tsaki domin dabbaqa tsari da kuma canza fasali ta hanyar koyarwar addinin musulunci.

Dr. Yusha,u Abdullahi Bichi
Deputy Director Public Relations

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *