June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malaman Islamiyya sun gudanar da wata zanga-zanga a nan Kano.

1 min read

Gamayyar Malaman Makarantun Islamiyya sun bukaci gwamnatin Kano data duba yuhuwar bude makarantun nasu musamman ma ganin cewa annobar corona ta dan yi sauki a jihar.
Jagoran Makarantun Malam Ibrahim Usman Umar ne ya bayyana haka a yayin wani gangami da suka gudanar a nan Kano.
Jaridar Bustandaily ta zanta Malam Ibrahim Usman Umar ya ce gwamnati ta bude gidajen kallon kwallon kafa Wanda nan ne ma ake samun cunkoso amma islamiyya babu maganar cunkoso.
Shima da yake jawabi sakataren gamayyar Malam Nuraddeen Muhammad Lawan cewa yayi dalibai sun watsar da karatunsu,Wanda sai an Kai ruwa Rana za’a iya dawo da abinda aka rasa.
A kan hakan ne kuma muka taba alli da Shugaban hukumar kula da makarantun Alqur’ani da islamiyya ta jihar Kano sheikh Gwani Yahuza Gwani Danzarga domin jin inda aka kwana game da makomar islamiyya tun bayan bullar annobar covid 19 ga kuma abinda yake cewa
Malaman sun rubuta doguwar mukala wacce take cewa ina makomar
karatun addini game da yara a lokaci na annoba da ake bukatar addu’ar yaran.
Anya gidan kallo da kasuwanni da komawa ma’aikatu sunfi karatun islamiyya kuwa mukalar kenan da suka rubutawa gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *