July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mohammed Umar ya zama sabon shugaban riko na EFCC

2 min read

An nada Mohammed Umar a matsayin sabon mukaddashin shugaban EFCC ne bayan dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar.

Sanarwar da Umar Jibrilu Gwandu, mai magana da yawun Ministan Shari’ar kasar Abubakar Malami ya fitar ranar Juma’a ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu daga mukamin mukaddashin shugaban EFCC nan take, domin kwamitin da shugaban ya nada ya gudanar da bincike a kansa ya samu damar yin hakan ba tare da shamaki ba.”

A cewar sanarwar, Shugaba Buhari “ya kuma amince daraktan ayyuka na EFCC, Mohammed Umar, ya karbi ragamar tafiyar da hukumar har lokacin da za a kammala binciken da ake yi da kuma umarni na gaba kan batun”.

Ranar Talata wata majiya mai karfi ta tabbatar wa BBC cewa ranar Litinin shugaban kasar ya dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar ta EFCC amma ba a fitar da sanarwa kan hakan ba sai yau Juma’a.

Binciken Magu: Ina makomar yaƙi da cin hancin Najeriya?
Ibrahim Magu: Shin shugaban EFCC zai bi sawun Lamorde, Waziri da Ribadu ne?
Osinbajo ya musanta karɓar biliyoyin naira daga wurin Ibrahim Magu
An dakatar da shi ne bayan ya bayyana a gaban wani kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa don bincike a kan cin hanci, sakamakon wani zargin da ake yi masa na ruf-da-ciki kan wasu kaddarori da aka kwace daga hannun mutanen da ake zargi da sata.

Kuma tun daga lokacin wasu rahotanni ke cewa an kama shi amma, kakakin hukumar EFCC da hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun musanta hakan, suna masu cewa gayyata aka yi masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *