September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Muna bincike don gano ranakun da aka fi yin fyaɗe a Kano – ‘Yan sanda

2 min read

Ta ce don haka za ta fara kama masu irin waɗanan kangwaye da suka gano an aikata fyade don tuhumarsu da taimakawa wajen aikata laifi.
“Mafi yawancin fyaɗen da ake yi, a kangwaye ake yin su” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan. “Kimanin kashi 33.3% na duk fyaɗen da aka yi a Kano”.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kashi 20.8% na fyaɗen da suka yi bincike kansu, an aikata su ne a gonaki da burtalai, Yayin da kashi 16.7% na fyaɗen a gidan waɗanda aka yi wa cin zarafin aka aikata su.
A cewar jami’in ɗan sandan daga watan Janairun 2020 zuwa yanzu, rundunar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe kan aikata fyaɗe guda 45, kuma tuni sun kama wasu da suke zargi har ma an gurfanar da su a gaban kotuna.
Abdullahi Haruna ya ce daga cikin mutanen, tuni kotu ta samu 27 da laifi, inda ta yanke musu hukuncin da ya haɗar da ɗauri har na tsawon shekara 14 da biyan diyya ga waɗanda aka yi fyaɗen.
Ya kuma ce suna ci gaba da gudanar da binciken, don tantance ƙaruwa ko raguwar aikata fyaɗe baya-bayan nan a cikin jihar Kano. “Yanzu binciken namu ma har ya kai, muna bibiyar waɗanne ranaku ne da awoyi aka fi yin wadannan laifuka na fyaɗe.
Mun kuma gano cewa mafi yawan waɗanda ake yi wa fyaɗe ɗin nan, sama da kashi 40 ana musu fyaɗe ne bayan an yaudare su da kuɗi ko abinci,” in ji jami’in ɗan sandan.
Ko a makon jiya sai da rundunar ‘yan sandan Kano ta gurfanar da wani mutum gaban kotu bisa zargin yi wa mata 40 fyade.
DSP Haruna ya ce a ko da yaushe suna shawartar mazauna unguwanni da suka ƙara sanya ido a kan take-take da kai-komon mutane a yankunan, da nufin kare ‘ya’yansu da kuma iyalansu.
Ya ce duk wani laifi da aka aikata a wani kango nan gaba sai sun gayyato masu ginin don ya yi ƙarin bayani.
“Wasu sukan bar kangwayensu ba tare da rufewa ba, za a bar kafar ƙofa, ba tare da an sa ƙyaure ba, ko a killace shi ta yadda ɓata-gari ba za su iya shiga ba,” in ji shi.
A baya-bayan nan dai, hankulan al’ummar Najeriya sun yi matuƙar tashi sakamakon ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu, musamman kan ƙananan yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *