September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Karota sun sha na jaki a hannun wasu sojoji

1 min read

VWata hatsaniya ta barke tsakanin jami’an sojoji dana hukumar lura da zirga-zirgar abubuwan hawa ta Jihar Kano Karota a dai-dai lokacin da ‘yan karotan ke tsaka da bada hannu a kan titin Dan Agundi.
Tun da fari wasu Sojoji ne guda biyu da ke cikin babur din adaidaita sahu ne suka baiwa doreban nasu umarnin wucewa duk kuwa da cewa jami’an karotan da ke bada hannu a girin sun tsayar da su, lamarin da jami’an karotan suka ce bazata sabu ba.
Hakan ce kuma ta harzuka Shaidun gani da ido sun shaidawa Bustandaily cewa sojojin sun farwa ‘yan karotan da duka ne a dai-dai lokacin da suka tsaya kai da fata cewa sojojin ba zasu wuce har sai danja ta basu hannu.
A kan hakan ne muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar lura da zirga-zirgar abubuwan hawan ta jihar Kano Karota,Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa inda ya tabbatar da faruwar lamarin,inda ya ce suna dakon rahoton jami’an yan sanda akan batun.
Ko a kwanakin baya dai an sami hatsaniya tsakaninsu ‘Yan korata da sojoji ko kuma ‘yan sanda sanda,wanda a sau da yawa hatsaniyar bata wuce kan bada hannu a kantituna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *