June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abu 10 da kuke buƙatar sani game da yawan al’ummar Najeriya

2 min read

Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ware ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara a matsayin Ranar Yawan Jama’a Ta Duniya.

Sakon MDD na bana dangane da ranar shi ne jan hankalin duniya kan batutuwan da ba a kammala cimma su ba wadanda aka amince da su a babban taronta na 1994 kan Yawa da ci gaban Al’umma.

Ana hasashen nan da shekara 80 yawan al’ummar duniya zai nunka, inda kasashe kamar Najeriya da ke da mutum muliyan 200 a yanzu, za ta kai kasa mai yawan mutum miliyan 728.vBBC ta yi duba kan wasu abubuwa 10 da watakila ba ku sani ba dangane da yawan al’ummar Najeriya.

Yawan al’ummar Najeriya a yanzu ya kai 206,214,251 kamar yadda bayanan Majalisar Dinkin Duniya suka nuna
Yawan jama’ar Najeriya ya kai kashi 2.64 cikin 100 na jumullar al’ummar duniya
Najeriya ce ta bakwai a jerin kasashen da suka fi yawan jama’a a duniya
Mutum 226 ke zaune a duk fadin murabba’in kilomita
Yawan fadin kasar Najeriya ya kai murabba’in kilomita 910,770
Kashi 52.0 cikin 100 na al’ummar kasar na rayuwa ne a birane, inda bayanai suka nuna cewa akwai mutum 107,112,526 da ke rayuwa a birane a shekarar 2020
Matsakaicin shekarun ‘yan Najeriya shi ne 18
Hukumar kidayar jama’a ta Amurka ta ce yawan al’ummar Najeriya zai zarta na Amurkar a shekarar 2047, inda a lokacin yawan mutanen Najeriya zai kai miliyan 379.25 million. A lokacin Najeriya za ta zama kasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya
MDD ta ce manyan dalilan da ke sa yawan jama’ar kasar ke karuwa su ne auren wuri da yawan haihuwa da rashin samun damar yin tsarin iyali
Duk mutum 1,000 suna haihuwar 37 a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *