June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana kokarin Bata min suna iji Magu

2 min read

Shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da aka dakatar a Najeriya Ibrahim Magu, ya gabatar da takardar korafi ga kwamitin dake binciken zarge zargen da ake masa kan yadda aka hana shi ganin takardar korafin da aka yi akan sa da kuma yadda kwamitin ke sauraron ba’asin shaidu ba tare da ambashi damar yi musu tambayoyi ba.

A wasikar da lauyan sa Wahab Shittu ya rubuta yace tun bayan tsare shi da aka yi ranar 6 ga watan nan, yake gabatar da bukatar ganin korafin da akayi a kan san a hada baki da azurta kai da amfani da ikon da ya wuce kima akan sa, amma har ya zuwa yanzu bai samu ba.

Shittu yace wanda yake karewa har ya zuwa yanzu bai san sharuddan da aka gindayawa kwamitin dake binciken ba da kuma abinda suke bukata, yayin da ya gabatar da korafi kan yadda ake tsare shi a ofishin Yan Sandan gudanar da bincike ba tare da bayyana masa laifin da yayi ba da kuma bashi damar kare kan sa.

Wasikar ta kuma yi korafi kan yadda aka mayar da shi kamar mai laifi, yayin da kafofin yada labarai ke cigaba da bata masa suna wajen yada labaran karya game da shi.

Daga cikin irin wadannan labaran, kamar yadda wasikar ta nuna, harda zargin ya baiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo naira biliyan 4 wanda Osinbajo ya musanta da gudanar da wasu asusun ajiya a boye da baiwa wasu na kusa da shi damar tafiyar da wasu harkokin sa da kuma sayen wasu kadarori a Dubai.

Lauyan yace wadannan zarge zarge sun yi matukar illa ga rayuwar wanda suke karewa da kuma ita kan ta Hukumar EFCC.

Shittu yace wadannan matakai sun mayar da Magu kamar wani babban mai laifin dake samun suka daga jama’a duk da yadda ya sadaukar da ran sa wajen yiwa kasa aiki a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *