July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Gombe za ta shuka sama da bishiyoyi miliyan ɗaya a 2020

1 min read

Gwamnatin jihar Gombe ta ƙaddamar da aikinta na shuka bishiyoyi karo na biyu a yankin Wajari da ke ƙaramar hukumar Yalmatu/Deba a jihar.

Gwamnan jihar ta Gombe Inuwa Yahaya ya ce ana shuka bishiyoyin ne domin kare muhallin jihar wanda rayuwar jama’a ta dogara a kai.

A cewarsa, shuka bishiyoyin zai taimaka wajen daƙile kwararowar hamada da gyara ƙasa da kuma dawo da inganci da martabar ƙasar noman da ke jihar.

Gwamnatin na da niyyar shuka akalla bishiyoyi miliyan ɗaya da dubu 200 a shekarar bana.

Gwamnatin jihar ta kuma ce za a fara shuka bishiyoyin a makarantu da asibitoci da tituna da wuraren aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *