June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar WHO Sun Isa China Don Fara Bicike Kan COVID-19

1 min read

Wata tawagar kwararru daga WHO hukumar lafiya ta duniya ta isa China don shirin fara bincike akan asalin annobar coronavirus.

Cutar da ke haddasa COVID-19, wadda aka yi imanin daga dabbobi ta fara kafin ta fara shafar bil’adama, a wata kasuwar sarin kayayyaki da tuni aka rufe ta a birnin Wuhan da ke tsakiyar China ta fara bulla a cikin shekarar da ta gabata.Wasu masana daga hukumar WHO da ke Geneva, da suka kware a fannin lafiyar dabbobi da nazarin yaduwar cututtuka a cikin al’umma, zasu gana da takwarorin aikinsu na China a Beijing ranar 11 ga watan Yuli don fidda sharudda da kuma abubuwan da zasu yi bincike akansu, a cewar Tarik Jasarevic, wani mai Magana da yawun hukumar WHO.

“Makasudin nazarin shine zurfafa bincike akan fahimtar dabbobin da cutar COVID-19 ta fara kamawa da kuma yadda dabbobin suka sanya wa mutane cutar, a cewar Jasarevic a wata hira da Muryar Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *