July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar dattawan Najeriya ta ce su ba ‘yar amshin shata ba ce

2 min read

Shugabn majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan, ya musanta ikirarin da wasu yan kasar ke yi na cewa majalisar da yake shugabanta yar amshin shatar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ce.

Sanata Ahmad Lawan ya shaidawa BBC cewa wasu daga cikin bukatun gwamnati da ake ganin suna amincewa da su, kamar maganar ciyo bashi dole ce kawai ta sanya, saboda babu isassun kudi a baitulmalin Najeriya.

”Ko kada mu dauki bashi, mu zauna ba mu da komai na ci gaba, ko kuma mu duba inda za a samu basussuka masu saukin ruwa, masu dogon lokaci kafin a biya, sai a ce kar a yi ?” Ya tambaya.

Ya kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kudurin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da suka hadar da gina hanyoyi da samar da titunan jirgin kasa a sassan kasar, sai dai ba ta da isassun kudi.Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen da za ta karɓo rancen biliyoyin daloli ne domin cike gibin kasafin kuɗin musamman yadda annobar korona ta katse mata hanzari da kuma ƙalubalen da Najeriyar ke fuskanta ta fuskar kudin-shiga, sakamakon faɗuwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi zargin cewa bashin da gwamnatin APC ke ci ya wuce kima – zai iya jefa Najeriya cikin wahala.

Duk da haka majalisar dokokin Najeriya ta amince da buƙatar, da za ta bai wa gwamnati damar karɓar rancen fiye da dala biliyan biyar, bayan a watan Afrilu majalisar ta amince ta karɓo rancen naira biliyan 850 a cikin gida.

Amma PDP da wasu masana na sukar yawan rancen na shugaban ke yi wanda suke cewa yana tattare da hatsari ga makomar ƙasar

Ita dai majalisa ta takwas da ta wuce karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ta sha yin fatali da bukatar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciwo basussuka.

Daya daga ciki ita ce watsi da bukatar gwamnatin ta karbo bashin dala biliyan 30 domin gudanar da wasu manyan ayyuka a shekaru biyu, bayan shugaban ya nemi amincewar majalisar domin ranto kudaden daga kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *