June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ministan shari’ar Jamhuriyar Congo ya ajiye muƙaminsa

1 min read

Ministan Shari’a na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya yi murabus daga mukaminsa lokacin da ake tsaka da rikin kan wata doka ma masu suka suka ce za ta rage karfin ikon bangaren shari’a.

Celestin Tunda bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba, amma ya samu kansa a tsaka mai wuya na rikicin da ke faruwa tsakanin shugaban kasar Felix Tshisekedi da kuma wanda ya gabace shi tsohon shugaban kasar Joseph Kabila.

Duk da ya bar kan mulki a zaben da ya gabata, Mista Kabila na ci gaba da jan akalar kasar saboda jam’iyyarsa ce ke da ‘yan majalisa mafiya rinjaye da yawan mukamai a gwamnatin kasar.

Magoya bayan shugaba Tshisekedi sun ta fitowa zanga-zangar rashin amincewa da sauye sauyen da Mista Kabila ke iza wutar kawo su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *