April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum biyar sun mutu a wani rikici

1 min read

‘Yan sanda a Afrika Ta Kutu sun ce an kashe mutane biyar yayin wata garkuwa da aka yi da wasu mutane a wata coci da ke wajen birnin Johannesburg.

Masu shiga tsakanin sun halarci cocin ta International Pentecostal Holiness da ke Zuurbekom a yammacin Rand.

Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa wani rikicin shugabanci ne ya barke a cocin.

‘Yan sanda sun ce sun kama mutum talatin da ake zargi tare da kwace gwamman makamai.

Hotunan da aka nuna sun hadar da na bindigogi da kuma wasu sauran makamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *