July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Malamai da Iyayen yara zata kalubalanci Ministan Ilimi kan Jarabawar Waec

1 min read

Kungiyar malamai da iyayen yara ta kasa NAPTAN ta ce za ta yi wata ganawa ta musamman da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu a gobe litinin don neman karin haske kan dalilan da suka sanya gwamnatin tarayya ta ce daliban kasar nan ba za su rubuta jarabwar kammala makarantun sakandire ta yammacin afurka a wannan shekara ba.

Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Haruna Danjuma ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce kungiyar ta damu matuka kan matakin da gwamnatin ta dauka na hana daliban kasar nan rubuta jarabawar ta WAEC a bana.

Tun farko dai hukumar ta WAEC ta ce za ta gudanar da jarabawar ce a ranar hudu ga watan gobe na Agusta, sai dai gwamnatin ta ce sakamakon ci gaba da yaduwar cutar covid-19, daliban kasar nan ba za su rubuta jarabawar ba a bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *