Mutane Miliyan Saba’in za su fada yunwa a cewar majalisar dinkin duniya
1 min read
Majalisar dinkin duniya ta ce za a samu karin akalla mutane miliyan saba’in da daya a sassa daban-daban na duniya, wadanda za su fada kangin talauci sakamakon cutar covid-19.
Wannan na cikin wani rahoto ne da sashen kula da tattalin arziki da walwalar al’umma na Majalisar dinkin duniya ya wallafa.
Rahoton ya ce kasashe da ke yankin kudancin nahiyar asiya da wadanda ke yankin kudu da hamada sahara a nahiyar afurka, sune zasu fi dandana kudarsu.
A cewar rahoton kasashen kudancin nahiyar asiya za su samu karin matalauta miliyan talatin da biyu, yayin da takwarorinsu da ke kudu da hamad sahara a nahiyar afirka, za su samu karin mutane miliyan ashirin da shida da za su fada kangin talauci saboda cutar ta covid-19.
A cewar Majalisar dinkin duniya wannan rahoton sashen ta da ke kula da tattalin arziki da walawalar al’umma da kuma wasu kwararru guda dari biyu ne da kuma kungiyoyi arba’in suka gabatar da wannan bincike.