July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 664 Suka Kamu da COVID-19 a Najeriya Ranar Asabar

1 min read

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya karu a cewar hukumar NCDC mai kula da dakile yaduwar cututtuka ta kasar.

Hukumar ta bayyana cewa an samu rahoton mutum 664 da aka tabbatar sun kamu da cutar a ranar Asabar 11 ga watan Yuli, gaba dayan adadin a Najeriya yanzu ya kai 31,987.

Cikin jihohi 18 da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar, jihar Lagos ce kan gaba da mutum 224, sai 105 a birnin Tarayya Abuja, 85 a Edo, 64 a Ondo, 32 a Kaduna, 27 a Imo, 19 a Osun.Sauran jihohin sun hada da Oyo, Plateau, Ogun da kowannensu aka samu mutum 17. Sai kuma mutum 14 a Rivers, 11 a Delta, 10 a Adamawa, 7 a Enugu, 6 a Nasarawa, 3 a Gombe, 3 a Abia, 3 a Ekiti.

Sanarwar da hukumar ta fidda a shafinta na Twitter ta kuma ce ya zuwa yanzu mutum 13,103 suka warke bayan haka mutum 724 suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *