July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Norwich City Ta Fadi Daga Gasar Premier

1 min read

Kungiyar ta fadi daga gasar ne bayan da West Ham ta ragargaza ta a cikin gidanta da ci 4-0 a wasansu na gasar ta Premier a yau Assabar.
Wannan ne karo na 5 da ake yin waje-road da kungiyar ta Norwich daga babbar gasar ta Premier, inda a yanzu za ta koma fafata gasar Championship ta Ingila a kakar wasanni mai zuwa.
Kungiyar ta sha kashi a wasanni 7 a jere na baya-bayan nan wanda ya kai ga ficewar ta daga gasar, a yayin da ta ke da tazarar maki 13 kasa da layin faduwa daga gasar, tare da wasanni 3 kacal da suka rage. Hakan na nufin ba yadda za’a yi ta tsira daga faduwa.
A yanzu za’a iya cewa Norwich din ta yi sunan faduwa daga gasar Premier, kasancewar ta fadi sau hudu a can baya a shekarun 1995, 2005, 2014 da kuma 2016.
To sai dai a bangare daya, kungiyar Watford ta kara samun kwarin gwiwar tsallakewa domin ci gaba da gaba da fafata gasar ta Premier, bayan da ita kam ta yi waiwayen baya ta doke Newcastle da ci 2-1 a yau Assabar.
Yanzu haka kuma kungiyar ta na saman layin faduwa daga gasar ne da tazarar
maki 6.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *