April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Shugaban kasar Mali na neman sulhu da masu zanga-zanga

2 min read

A kokarin shawo kan zanga-zangar da ake fama da ita, Shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubakar Keita, ya ce za a sake gudanar da zabukan ‘yan majalisar da ake ganin suna dabaibaye da rikici.
A watan jiya ne yankin yammacin Afrika mai kawance da ECOWAS ya yi kira da asake gudanar da zabukan.
A wani bayani da ya yi ta talabijin, a ranar da aka ce an kashe akalla mutum hudu masu zanga-zanga, Shugaba Kaita ya soke kotun kundin tsarin mulkin kasar, yana cewa ya yanke hukuncin amfani da shawarwarin da ECOWAS ta ba shi.
Zanga-zangar da ake yi a Mali ta nuna kai wa makura ce kan sukar yadda gwamnati ke tafiyar da sha’anin tattalin arzikin kasar da kuma rikicin masu ikirarin jihadi.
An bude iyakar Syria da Turkiyya domin kai agaji
Kungiyoyin da ke aiki agaji a arewa maso yammacin Syria sun ce matakin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na barin iyakar Syria da Turkiyya a bude domin kai kayan agaji zai iya janyo asarar rayuka.
Kwamitin sulhun ya gabatar da wata kuri’a ne a daren jiya ta ganin an bar iyaka daya a bude ta mashigar Turkiyya zuwa yankin Idlib wanda ke karkashin ikon ‘yan tawaye, bayan China da Rasha sun yi duk kokarin ganin an samu iyakoki biyu a bude.
A wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin ba da agajin suka fitar sun ce damuwarsu kan mazauna yankin ce da suka kai kimanin miliyan daya da dubu 300 wadanda kuma dukkansu sun dogara ne kan abinci da maganin da Majalisar Dinkin Duniya ke kai wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *