July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Sojojin Najeriya sama da 350 za su ajiye aikinsu’

2 min read

Sojojin Najeriya fiye da 350 za su ajiye aikinsu na soja saboda sun gaji da aikin bisa wasu dalilai na rashin gamsuwa da shugabancin rundunar sojin da kuma rashin karfafa masu ƙwarin guiwa.

Haka kuma ƙarancin albashi da rashin kayan aiki na daga cikin batutuwan da ƙananan sojojin da ke faɗa da Boko Haram suka koka akai.

Mai fafutikar kare haƙƙin bil’adama kuma mai bincike kan ƙungiyar Boko Haram Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa akwai wasu ƙarin sojojin ma da ke son barin aikin na soja amma har yanzu ba a amince da buƙatarsu ba.

A baya, rundunar sojin Najeriya ta dakatar da ba sojoji damar yin ritaya a duk lokacin da suka nema inda ake zargin wasunsu da zama matsorata da kuma yin zagon ƙasa yayin da suke sukar shugabancin rundunar sojin.

Sojojin na Najeriya za su ajiye aikin ne a farkon watan Janairun badi.
An shafe shekaru 10 Najeriya na fama da rikicin ƴan ta’adda na Boko Haram. Kuma rundunar Sojiin ƙasar ta sha iƙirarin cewa ta murƙushe ayyukan ƙungiyar amma kuma galibi a ɓangarenta ba ta cika bayyana irin giriman hasarar da ta yi ba.

Amma a zahiri maharan na ci gaba da da kai hare-hare kan sojoji da fararen hula, inda a farkon wannan makon aka bayar da rahoton cewa sojoji sama da 30 ne aka kashe a wani harin kwantan ɓauna na Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *