June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tattalin arzikin Afrika zai farfado a cewar AFDB.

1 min read

Bankin raya kasashen afurka AFDB ya ce, yawan matasa a yankin yammacin afurka, zai taimakawa yankin gaya, wajen farfadowa da koma bayan tattalin arzikin da yake ciki, duk kuwa da ci gaba da yaduwar cutar corona.

Hakan na cikin wani rahoto ne na shiyya-shiyya da bankin na AfDB ya fitar game da halin da yankin na yammacin afurka ke ciki, sakamakon cutar ta covid-19.

Bankin ya wallafa wannan rahoto ne gaban ministocin kudi na Najeriya Zainab Ahmed da takwararta na Ghana, Ken Ofori Atta.

Saboda haka bankin raya kasashen na afurka ya bukaci kasashe da ke yankin da su kara kaimi wajen ganin sun ci gajiyar yawan jama’a da suke dashi don bunkasa tattalin arzikinsu.

Babbar jami’ar kula da harkokin kasuwanci a ofishin bankin mai kula da yammacin afurka, Marie-Laure Akin-Olugbade, ta ce yammacin afurka na da dama na tserewa takwarorinsa, matukar yayi amfani da damar da ya ke da shi.T

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *