June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar WHO Ta Kaddamar Da Shirin Bada Rigakafin Malaria a Borno

1 min read

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta kaddamar da shirin bada rigakafin cutar masassarar cizon sauro da ake kira Malaria a garin Maiduguri da ke Arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da matsalar rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram.

Hukumar ta ce ta na sa ran samar da rigafin ga kananan yara akalla miliyan biyu a jihar Borno. A karshen makon da ya gabata ne jami’an hukumar suka kaddamar da shirin rigakafin a fadar mai martaba Shehun Borno Dr. Abubakar Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, inda aka bai wa wasu kananan yara rigakafin.

Mai martaban ya ce ya kamata jami’an hukumar ta WHO su mayar da hankali kan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cike da kananan yara. Ya kara da cewa akwai bukatar a zagaye cikin gari gaba daya domin a magance wannan cuta mai kisa.Mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Usman Kadafur, ya yi kira ga iyayen yara wajen bai wa ma’aikatan kiwon lafiya hadin kai domin ganin yaransu sun sami rigakafin.

Wani jami’in hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana irin muhimmancin wannan rigakafin musamman idan aka yi la’akari da zazzabin cizon sauro ga mata masu ciki da kananan yara a lokacin damina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *