June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 13,447 Suka Warke Daga COVID-19 a Najeriya

1 min read

Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa karin daruruwan mutane sun kamu da cutar COVID-19 wadda coronavirus ke janyowa.

A cewar hukumar, mutum 571 ne cutar ta harba a ranar Lahadi 12 ga watan Yuli, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 32,558.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 13,447 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 740 suka mutu.An samu sabbin alkaluman ne daga jihohi 20, har yanzu jihar Lagas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, yanzu ta sake samun mutum 152. Sai jihar Ebonyi da ke bin ta da mutum 108.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Edo-53, Ondo-46, Abuja-38, Oyo-20, Kwara-19, Plateau-17, Osun-14, Bayelsa-14, Ekiti-14, Katsina-14, Akwa Ibom-11, Kaduna-11, Rivers-11, Niger-10, Ogun-7, Kano-6, Cross Rivers-4, Bauchi-2.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *