September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sarkin Kano yayi nade-nade na farko tin bayan hawansa kan mulki.

2 min read

A baya dai, Sanusi Lamido Ado Bayero ne ke riƙe da muƙamin Ciroman Kano, wanda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya sauke saboda ya ƙi yi masa mubaya’a bayan zamansa sarkin Kano.

Hakan ta sa Sarki Sanusi ya maye gurbinsa da Nasiru Ado Bayero a matsayin Ciroman Kano, wanda yanzu shi ne Sarkin Bichi.

Tuni Sunusi Ado Bayero ya yi mubaya’a ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda hakan kamar wata sanarwa ce ga sarkin cewa ya dawo gida da zama.Wata sanarwa da Alhaji Sarki Waziri, Ɗan Rimin Kano ya aike wa Sakataren Gwamnatin Kano ta kuma tabbatar da naɗa Aminu Babba Ɗan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, wanda Marigayi Sarki Ado Bayero ya sauke daga muƙamin Sarkin Dawaki Mai Tuta shekara 16 da suka gabata.

A shekarar 2003 ne Ado Bayero ya sauke Aminu Babba daga sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma Hakimin Gabasawa sakamakon bijire wa umarnin da ya ba shi na bayyana a gabansa.

Marigayi Ado Bayero – mahaifin sarkin Kano na yanzu – ya kuma zargi Aminu Babba da laifin shiga harkokin siyasa da rashin ɗa’a ga Masarautar Kano.

Sai dai Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin da Masarautar Kano ta ɗauka na tuɓe rawanin Aminu Babba a ranar 5 ga watan Yuni bayan nasarar da ya samu a kotun Jihar Kano da kuma ta Ɗaukaka Ƙara.

Ya zuwa yanzu Masarautar Kano ba ta bayyana dalilin dawo da Aminu Babba Ɗan Agundi cikin masarautar ba a matsayin Sarkin Dawaki Babba kuma Ɗan Majalisar Sarki.

Sai dai wasu makusantan sarkin da ba su yarda a ambaci sunansu ba sun bayyana wa BBC cewa Sarkin Dawaki Babba sabuwar sarauta ce, wadda sarkin ke da ikon ƙirƙirowa ko arowa daga wata masarauta.

Suka ƙara da cewa irin hakan ta taɓa faruwa ga kawun sarkin Kano na yanzu – Aminu Ado Bayero – inda aka ƙirƙiri sarautar Barde Kerariya kuma aka naɗa Alhaji Kabiru Bayero.

Har yanzu gwamnatin Kano ba ta ce komai ba kan wasiƙar da masarautar ta Kano ta aike mata bisa buƙatar sarkin ta naɗa mutanen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *