June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ta Yiwu a Samu Ambaliyar Ruwa a Wasu Yankunan Najeriya – NEMA

1 min read

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya da ake kira NEMA ta yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi fiye da 100 a Najeriya.

A cikin wata sanarwar da shugaban hukumar NEMA, AVM Muhammadu A Muhammed ya fitar, hukumar ta shawarci mazauna yankunan da su yi kaura domin tsira da rayukansu da kuma dukiyoyinsu.

Kananan hukumomin da ake hasashen aukuwar ambaliyar sun hada da Kaura, Zaria, Kaduna North da ke jihar Kaduna, sai kuma jihohin da ke yankin kudu maso yammacin kasar da tuni har sun fara fuskantar matsalar ambaliyar.Wasu daga cikin mazauna birnin Lagos sun nuna damuwarsu, kuma sun yi kira ga hukumomi da ma mazauna yankunan da su fito a hada hannu da karfe wajen shawo kan wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *