Watakila kimar Manchester City ta zube a yau
1 min read
A yau Litinin Manchester City za ta san makomarta dangane da samun gurbi a gasar zakarun Turai, yayin da kuma kimarta ke fuskantar barazanar zubewa a duniyar tamaula.
Wani lokaci a yau din ake sa ran Kotun Sauraren Korafe-korafen Wasanni, wato CAS za ta sanar da hukuncin da ta yanke kan Manchester City bayan zaman sauraren karar da kungiyar ta daukaka a cikin watan Yuni.
A cikin watan Fabairu ne Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta samu kungiyar da laifin karya ka’idojin kashe kudade, abin da ya ta haramta mata shiga gasar zakarun Turai na shekaru biyu tare da cin ta tarar Euro milyan 30, amma Manchester City din na kalubalantar wannan hukuncin.
Yanzu haka, kungiyar na fatar kotun ta CAS za ta wanke ta daga laifin da aka ce ta aikata, lamarin da zai sa a janye hukuncin haramta mata shiga gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Amma muddin kungiyar ta gaza samun nasara a yau din, to babu shakka hukuncin haramcin shiga gasar ta zakarun Turai zai kasance daram, sannan kuma kimarta za ta zube.