July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yar Nelson Mandela Ta Rasu

1 min read

Kafar yada labaran kasar ta SABC ta sanar cewa Mandela ta mutu a wani asibiti da ke babban birnin Afirka ta Kudu amma basu bayyana sanadin mutuwarta ba.

Jam’iyyar African National Congress mai Mulki wanda mahaifinta ya jagoranta a gwagwarmayar kawar da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudun ce ta tabbatar da mutuwarta.A shekara ta 1985 Zindzi ta yi fice, lokacin da ta karanto wasikar da mahaifinta ya rubuta ta kin amincewa da sharadin samun ‘yancin kai da shugaba P.W. Botha ya bayar na ANC ta watsi da dabarunta masu tsauri akan nuna addawa ga wariyar launin fata.

Mandela na aiki a matsayin jakadiyar Afirka ta kudu a kasar Denmark a lokacin da ta mutu.

Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor, ta yabawa Zindzi Mandela tana mai cewa ”a matsayinta na diyar gwarzon gwagwarymaya Tata Nelson da Mama Winnie, ita kanta jaruma ce a fagen gwagwarmaya. Ta yi wa Afirka ta Kudu aiki sosai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *