June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a bude Makarantu bisa wasu sharadai iji Adamu- Adamu

1 min read

Gwamnatin tarayya ta shimfida wasu sharudda da ta ce sai bi su ne sannan za a bude makarantu a dukkannin matakai a kasar nan.
Wata sanarwa da ma’akatar ilimi ta tarayya ta fitar yau a Abuja mai dauke da sa hannun ministan ilimi Malam Adamu Adamu da kuma karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ta ce wajibi ne a dauki wannan mataki na shimfida ka’idojin domin kare daliban daga kamuwa da kwayar cutar Covid-19.
Cikin sharuddan akwai bayar da tazara tsakanin daliban, da samar wuraren tsaftace hannu masu inganci, domin cika ka’idojin da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *