June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Kullum Ana Yi Wa Mutane Akalla 15 Fyade a Kaduna – Alkali Bello

1 min read

Babban alkalin alkalai a jihar Kaduna, Muhammad Lawal Bello ya bayyana cewa a kowace rana ana yi wa akalla mutane 15 fyade a jihar.

A yayin wani taron lauyoyi da kungiyar lauyoyin Najeriya ta NBA ta shirya a Kaduna, ya jaddada yadda adadin wadanda ake yi wa fyade ke dada karuwa. Ya ce “yawancin wadanda ake yi wa fyaden yara ne ‘yan tsakanin watanni uku da shekaru 12.”

“Yadda adadin yaran da ake batawa abin ban tsoro ne, kuma dole sai an hada hannu an kuma dauki mataki domin a kawo karshen wannan matsala.” In ji Alkalin.

Ya kara da cewa, annobar Covid-19 ta tilastawa fannin shari’a gudanar da shari’o’inta ta kafar intanet domin kaucewa jan lokaci wajen kwato wa wadanda aka yi wa fyade ‘yancinsu.

A karshe ya bayyana cewa shari’o’i masu tsauri da za su iya kai ga daure mutum gidan yari da hukuncin kisa, za a kaucewa yin su ta Intanet saboda muhimmancin bayyanar shedu a gaban kotu.

Hakan duk na zuwa a lokacin da ake ta fuskantar karin adadin wadanda ake yi wa fyade a Najeriya, musamman kananan yara da mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *