June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An zartar da daurin rai da rai ga masu garkuwa da Mutane a Nigeria.

1 min read

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.

A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ga mutanen da aka kama da laifini.

Haka kuma majalisar ta soke bambanci jinsi maza ko mata kan laifin fyade.

Wannan matsaya da majalisar da cimma ta biyo bayan tsallake karatu na uku da kudurin ya yi tare da sauya dokar manyan laifuka ta kasar, ta 2004.”

Dan majalisa da ke wakiltar jihar Legas ta tsakiya Sanata Oluremi Tinubu ne ya nemi a kara tsaurara dokar da kuma cire banbanci a tsakanin jinsi a lokacin hukunci kan fyade.

Kudurin ya cire wa’adin gabatar da kara kan cin zarafi a kasar baki daya.

Idan kudurin ya zama doka, hukuncin cin zarafin zai zama za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *