Ibrahim Magu ya sake gurfana gaban kwamitin fadar shugaban Kasa.
1 min read
dakataccen mai rikon mukamin shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC Ibrahim Magu ya sake bayyana a gaban kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa masa karkashin jagorancin Justice Ayo Salami.
Tun a ranar litinin din da ta gabata ne aka fara gudanar da zaman kwamitin a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa da ke Villa a Abuja.
Kuma tun makon jiyan ne dai yake hannun jami’an ‘yan sanda, bayan dajami’an tsaro na farin kaya DSS suka cafke shi lokacin da yake dab da shiga ofishinsa a Abuja.
To sai dai an hana ‘yan jarida shiga dakin taron.