June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Likitoci 35 sun kamu da Corona a Jiya Litinin

1 min read

Kungiyar likitoci ta kasa ta ce mambobinta 35 ne suka kamu da kwayar cutar Covid-19 a Jihar Kwara, tun bayan bullar cutar a Jihar.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Kwara Dr Kolade Solagberu ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Ilori, kan babban taron kungiyar na shekara-shekara na bana.
Dr Kolade Solagberu ya ce babu rahoton mutuwar likita ko da guda, amma ya ja hankalin al’ummar Jihar da su kaucewa yadda da masu yada labarin cewa cutar Covid-19 ba gaskiya ba ce, yana mai cewar har sun ba da hadin kai ne sannan za a samu nasarar kawar da cutar a Jihar.
Ya kuma shawarci mutane su kaucewa ziyartar asibitoci ba tare da kwakkwaran dalili ba, don kaucewa yaduwar cutar, har ma ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa yadda ta rufe makarantu a kasar nan don hana bazuwar cutar.
Mutane 401 ne suka kamu da cutar a jihar Kwara inda aka sallami 179 daga cibiyar killace masu fama da cutar bayan sun warke, yayin da 14 suka riga mu gidan gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *