June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Dokokin Katsina ta fara binciken gwamnatin jihar kan zargin Wadaka da kudade

1 min read

Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Katsina da ke area maso yammacin Najeriya da aka kafa ya fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa gwamnatin jihar na almubazzaranci da maƙudan kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 52.

Waɗansu kungiyoyin farar hula ne suka buƙaci majalisar da ta gudanar da binciken bayan wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Mahdi Shehu ya bijiro da zargin.

Hon Abduljalal Runka, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya shaida wa BBC cewa sun shiga binciken ne da zummar hukunta gwamnatin idan an same ta da laifi ko kuma hukunta Alhaji Mahdi Shehu idan ƙazafi ya yi mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *