June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

N-Power: An kusa rufe shirin amma matasa kusan miliyan biyar ne suka mika takardunsu – Sadiya

2 min read

Minista a ma’aikatar bayar da agaji da ayyukan gaggawa Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter.

“Kwana 16 ke nan tun da aka bude shafin da ake karbar takardun neman aikin kuma kawo yanzu mun samu takardu miliyan 4.48”, a cewar ministar a sakon da ta wallafa ranar 12 ga watan Yuli.Ta kara da cewa ita da ma’aikatanta suna aiki tukuru wajen ganin shirin ya tafi kamar yadda ya kamata.

Ranar 26 ga watan Yunin 2020 aka bude shafin neman aikin na N-Power wanda za a dauki mako shida aka karbar takardun neman aikin matasa.

Shirin na N-Power ya fada cikin rudani bayan da a farkon watan nan majalisun tarayya a Najeriya suka dakatar da shirin wanda gwamnatin ƙasar ta ci alwashin ɗaukar ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi 774,000 har sai sun samu cikakken bayani kan tsarin ɗaukar mutanen da za su ci gajiyar shirin.Matakin ya zo ne kwana guda bayan ƙaramin ministan kwadago Festus Keyamo ya yi zazzafar jayayya da ‘yan majalisar lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi da shi a watan jiya.

Sai dai su kansu ‘yan majalisar ana zarginsu da babakere a kan shirin, ko da yake sun musanta.

Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama’ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito.

Haɗin gwiwar majalisar ƙwadagon ya buƙaci sanin hanyar da aka bi aka zaɓo ayarin mutum 20 daga kowacce jiha a Najeriya don yin aikin tantance mutanen da za a ɗauka aikin na wucin gadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *