June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Ma’aikatan KEDCO sun Mutu.

1 min read

Wasu ma’aikatan kamfanin rarraba wutar lantarki shiyyar Kano KEDCO guda biyu sun rasa rayukan su sanadiyyar hatsarin mota da ya rutsa da su ta hanyar su ta dawowa Kano daga jihar Katsina.
Hakan na cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya fitar.
Sanarwar ta ce, wadanda suka mutun sun hada da Malam Nazir Ahmad da Malam Abdurra’uf Ahmad.
Sanarwar ta kara da cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar a karamar hukumar Kankiya wanda yayi sanadiyyar hatsarin, tare da jikkata mutane shida yayin da direban motar da wani guda mai suna Mr Johnson suka tsira ba tare da raunuka ba.
Kazalika sanarwar ta bayyana cewa tuni aka debo gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Kano, wadanda kuma suka jikkatan an kai su zuwa asibiti don ci gaba da duba lafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *