September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan bindiga ‘sun sace akalla mutum 30’ a Kaduna

3 min read

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya, na cewa wasu `yan bindiga sun sace akalla mutum 30 a yankin Danbushiya da ke karamar hukumar Chikun.

Kazalika `yan bindigar sun kashe mutum daya daga cikin wadanda suka sace bayan ya yi runkurin tserewa.

Wasu mazauna yankin, sun bayyana cewa lamarin dai ya faru ne tun a ranar Lahadin da ta wuce da daddare, a lokacin da mazauna kauyukan da ke kewaye suke ribibin komawa gida.

Wani mazaunin yankin ya ce `yan bindigar sun badda-kama ne ta hanyar sanya kayan damara, sannan suka datse wata babbar gadar da ke kan hanyar da ta hada garuruwan yankin da unguwar Millenium City da kuma garin Kaduna.

Ya ce: “Wadannan mutane suna sanye ne da kayan sojoji, wasu kuma suna sanye da kayan `yan sanda. Kuma sun tsaya a hanya n suna tambayar face-mask. In sauka tambaya ina face-mask din ka, idan babu sai ce ka yi nan.”

“Da ma sun rabu biyu ne. wasu suna kan hanya wasu suna gefe. In ka tafi wurin wadanda suke gefe sai su sa ka ka kwanta. Sun yi ta`adi sosai. Har sun harbi mutum daya, nan take ya rasa ransa. Kuma sun tafi da mutane. Har zuwa yanzu dai ba mu san adadin mutanen da suka tafi da su b a. Wannan da suka kashe ma, lokacin da ya fahinci ba jami`an tsaro ba ne ya yi yunkurin ya gudu, sai suka harbe shi nan take.

Sai dai mutanen yankin sun bayyana cewa jami`an tsaro sun hanzarta wajen kai dauki, kasancewar ganin su ma ya sa `yan bindigan suka bazama daji.

Amma duk da haka sai da suka tafi wasu daga cikin mutanen da suka kama.

Wannan lamari dai, kamar yadda wani mutum ya ce ya tayar da hankalin mazauna yankin.

“Gaskiya al`umar wannan wuri muna cikin dardar, kasantuwar ba a taba samun da ya faru irin wannan ba a a wannan yankin. Yanzu tun kafin karfe hud z aka wani yana neman ya dawo gida. Har yanzu dai mutane suna cikin halin firgici. Gonakinmu, kasan saboda faruwar irin wannan abun ba a iya zuwa gonaki masu nisa sai na kusa da gari irin su Danbushiya da da dokan maijama`a nan ake zuwa. To dalilin faruwar wannan abu mutane ma sun kaurace wa gonakin nasu. Rokon da muke so mu yi ga hukumomi shi ne a kara zage-dantse wajen ganin an yi tattalin zaman lafiya a wajen nan.

Har zuwa dai `yan bindigar ba su waiwayi `yan uwan mutanen da suka sace ba, ballantana a kai maganar fansa.

Mun tuntubi kakakin rundunar `yan sanda a jihar Kaduna ta waya, amma ba mu yi nasara ba.

Kazalika babu wata sanarwa ta bangaren gwamnatin jihar game da wannan satar mutane da `yan bindiga suka yi.

Kodayake mahukunta a da jami`an tsaro sun sha yin alwashin bakin kokarinsu wajen kare rayuka da dukiyar jama`a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *