June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tebura dari da hamsin Karota da rushe a Kasuwar Sabon Gari a yau Labara

2 min read

Yan tebura dake kasuwar Abubakar Rimi wacce akafi sani da kasuwar Sabon Gari sun bukaci Gwamnatin jihar Kano data kawo musu dauki a bisa umarnin tashi daga guraren kasuwancin su da jami’ar Karota suka basu wa’adin yau Labara 15 ga watan Yulin 2020.

A cewar ‘yan kasuwar sama da shekara 20 suna gudanar da kasuwancinsu a wadannan gurare,amma yanzu lokaci daya kawai suka sako daga Karota cewa su bar guraren.Alhaji Saminu Abubakar Gaya shi ne jagoran ‘yan kasuwar ya shaida mana cewa tsahon lokaci suna gudanar da kasuwancin nasu,kuma duk wata ka’ida da hukumar kasuwar ta shinfida suna bi,amma yanzu jami’an Karota suna neman ra basu da gurin neman abincin su.

Suma wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun bukaci sarkin Kano Aminu Ado Bayaro da kuma Gwamnatin Kano data duba wannan lamarin nasu.

Jin koken ne kuma ya sanya jaridar Bustandaily tuntubi hukumar Karota domin Jin hanzarin su game da wannan lamari.
Alhaji baffa Babba Dan Agundi shi ne shugaban hukumar lura da zirga -zirgar abubuwan hawa ta jihar Kano karota ya ce dukkak ‘yan kasuwar da suke gudanar da kasuwancin su akan hanyoyi ba bisa ka’ida ba dama tini suka basu wa’adin wasu kwanaki dasu tashi wanda wa’adin zai kare a Laraban nan.
Ida ya ce hatta titina suma sun kara zana sababbin layi wanda yake nunawa kowa ka iya iyakarsa.

Yan kasuwar dai sun ce kamata yayi a inganta kasuwancin nasu,musamman ma ganin yadda annobar Covid 19 ta haifar musu da a sarar dukiya mai yawa,sai gashi kuma ana kokarin rabasu da kasuwancin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *