July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An dakatar da makusantan Magu daga aikin EFCC

2 min read

Binciken da ake ci gaba da yi wa tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC da aka dakatar a Najeriya, Ibrahim Magu kan zargin almundahanar kudade, ya soma shafar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar, abin da ya kai ga dakatar da sama da 11 daga cikinsu.

TALLA

Rahotanni sun ce, akalla manyan jami’an hukumar ta EFCC 11 aka dakatar, cikinsu har da babban sakatarenta Olanipekun Olukoyede, sai kuma wasu shugabannin hukumar yakar rashawar na shiyya-shiyya da kuma shugabannin sashin hukumar ta EFCC na shari’a, da na sa ido kan binciken laifukan kin biyan haraji, kamar yadda majiya mai tushe da ta nemi sakayata ta tabbatar.

Mafi akasarin manyan jami’an da aka dakatar sun sha bayyana a gaban kwamitin da ke bincikar tsohon shugabansu Ibrahim Magu, bisa zarge-zargen da ake masa na almundahana.

Har yanzu dai Magu na ci gaba da fuskantar bincike gami da amsa tambayoyi daga kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara na kasar, Ayo Salami.

Ranar litinin ta makon jiya aka tsare Ibrahim Magu gami da gurfanar da shi gaban kwamitin binciken, inda ake ci gaba da laluben gaskiyar lamari kan tuhume-tuhumen saba ka’idojin aiki, da karkatar da kudaden da ake yi wa tsohon shugaban hukumar ta EFCC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *