June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Fara Binciken Wasu Kudaden Fasho Da Suka Yi Batan Dabo

2 min read

Gwamnatin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce ta bankado wata muguwar sata da aka tafka har ta Naira miliyan dubu biyar da miliyan dari bakwai a ma’aikatar kula da harkokin tsofaffin ma’aikata da suka yi ritaya a jihar da ake kira Fansho, ko da yake ya zuwa yanzu gwamnatin ba ta ayyana sunayen wadanda ake zargi ko tuhuma da sace wadannan makudan kudaden ba.

Babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin Fanshon jihar Neja, Alhaji Usman Tinau, ya ce akwai mutane 15 da ake tuhumarsu kan sace wadannan kudade kuma gwamnati za ta yi duk abin da ya dace wajan ganin ta kwato wadannan kudade na jama’a da suka bauta wa kasa.

Tinau ya kara da cewa tuni suka fara kirawo wadanda a ke zargi da yin sama da fadi da kudaden domin su amasa wasu tambayoyi.

Musa Madaki Kusharki, daya daga cikin tsofaffin ma’aikatan jihar Neja ya ce yanzu kusan shekarar sa hudu da yin ritaya amma har yanzu kudinsa na fansho ba sa shiga hannunsa yadda ya kamata.

Sannan ya kara da cewa hakika idan Allah ya yarda duk wani mai karbar Fansho ko mai ritaya a jihar Neja zai yarda cewa gwamnati ta tashi tsaye wajan yaki da cin hanci da rashawa.

A halin da ake ciki yanzu, gwamnatin jihar Neja ta ce ta amince da sabon tsarin Fansho a jihar, al’amarin da ke bukatar wayar da kan ma’aikatan domin su fahimce shi sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *