April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Tafka Muhawara Kan Tsawon Wa’adin Daurin Masu Garkuwa Da Mutane

2 min read

Dokar dai a da ta ce duk wanda yayi garkuwa da mutane za a daure shi har tsawon shekara 10 ne a gidan yari, amma Majalisar Dattawa ta mayar da dokar zuwa daurin rai da rai ga duk wanda laifin yin garkuwa da wani ya tabbata akansa.

Dama wanan dokar na kunshe ne da hukunce-hukunce da suka shafi wadanda suka yi garkuwa da mutane ne da kuma wacce aka yi wa fyade da ta kai kara cikin wani takaitaccen lokaci.

Yanzu an sabunta dokar inda za a zartas da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda yayi garkuwa da mutane a maimakon shekaru 10 a da. Bayan haka an sauya matsayin dokar na cewa mata kadai ake yiwa fyade, yanzu dokar ta hada da maza.

Kwararre kan harkokin tsaro Dakta Kabir Adamu ya ce wannan doka za ta taimaka gaya wajen rage yawan yin garkuwa da ake yi da mutane wanda a yanzu har talaka ma bai tsira ba, “wani abin takaici kuma wani zubin ma sai an karbi kudin fansa sai kuma a kashe mutumin da aka yi garkuwa da shi.”

Shi ma kwararre a Fannin zamantakewa, Adam Abubakar Aliyu ya ce yana murna da wannan kokari da Majalisar Kasa ta yi domin yin wanan doka ya nuna cewa sun damu da halin da ‘yan kasa ke ciki.

To sai dai ga Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta Arewa Sanata Ahmed Babba Kaita, ya ce “da so samu ne a mayar da hukuncin garkuwa da mutane ya zama kisa kai tsaye” domin a ganinsa an taba gwadawa a wasu kasashe irin su Indiya, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba sai da suka mayar da dokar ta zama ta kisa sannan kasar ta samu lafiya.

Yanzu dai za a tura dokar ne zuwa ga Majalisar Wakilai domin ta amince da ita kafin a kai wa Shugaban kasa ya rattaba hannu akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *