June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babu ruwanmu wajen tsare Magu-‘Yan sandan Najeriya

1 min read

Babban Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya ce babu hannun rundunar ‘yan sandan kasar wajen kama shugaban hukumar EFCC da aka dakatar Ibrahim Magu da kuma tsare shi.

Adamu ya bayyana haka ne a wasikar da ya rubuta wa lauyan Magu, Tosin Ojaomo bayan ya bukaci a bada shi beli dangane da tsare shi da aka yi a ofishin ‘yan sandan da ke Abuja.

A wasikar da Sufeto Janar din ya rubuta wa lauyan mai dauke da sanya hannun babban hafsansa Idowu Owohunwa, Adamu ya bukaci lauyan Magu da ya tuntubi kwamitin da shugaban kasa ya kafa da ke gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa dakataccen shugaban na EFCC.

Sufeto Janar din ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta gudanar da bincike kan Magu ba kuma babu hannunta a tsare shi da aka yi.

Tuni aka sallami Magu a yammacin Laraba bayan kwashe ‘yan kwanaki a tsare saboda zargin sa da handame wasu kudade da kadarorin da EFCC ta kwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *