June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar ICPC Ta Kai Ziyara Jihar Kebbi Don Bibiyar Wasu Ayyuka

2 min read

Wasu lokuta a kan samu matsaloli wajan aiwatar da ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayyar Najeriya ke ba ‘yan majalisar dokokin tarayya domin su yi wa al’umomi a mazabunsu, matsalolin kuwa sun hada da ko dai kin yin aikin, ko karkatar da akalar kudin aikin, ko kuma yin aiki mara inganci.

Wasu jami’an hukumar yaki da cin hanci da aikata ba daidai ba a shiyar Sokoto (wato ICPC a takaice) sun kai ziyara jihar Kebbi domin bibiyar irin wadannan ayyuka da aka yi a shekarun da suka gabata don ganin ko ana yin su bisa ka’ida ko a’a.

Shugaban hukumar ICPC Shiyyar Sokoto, Akibu Garba, ya ce suna binciken ayyukan da ‘yan majalisun dokokin tarayyar suka yi na kudi sama da Naira biliyan uku, ciki har da gina asibitoci, makarantu, da kuma rijiyoyin burtsatse.

Sannan ya kara da cewa makasudin wannan bincike abu guda uku ne, don ganin ko an yi aikin, ko an yi shi daidai yadda ya kamata, kuma ya na anfanar jama’a?

Masanin harkokin tattalin arziki Dr. Rufa’i Shehu na jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce da hukumar ICPC ta gudanar da wannan aikin a shekarun baya da yanzu talakawan Najeriya sun wadatu da samun wasu ayyukan raya kasa.

Su ma jama’ar jihar Kebbi sun ce wannan mataki na jami’an ICPC ya na da kyau kwarai da gaske saboda duk ayyukan suna bukatar a rika duba su, inda ya kamata a yi gyara kuma a gyara.

Hukumar ta ICPC ta ce duk inda ta ga ana aikata ba daidai ba ta na bincikar ‘yan kwangila da kuma hukumar da ta bayar da aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *