June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kamfanin Najeriya ya fara daukar nauyin gasar Kenya

1 min read

Kamfanin cacar yanar gizo na Najeriya Betking ya zama sabon mai daukar nauyin gasar firimiya lig ta kasar Kenya a karkashin wata hadaka ta zunzurutun kudi har Dala miliyan 11.

Wannan hadakar za ta ci gaba da aiki har zuwa shekarar 2025 kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Kenya ta sanar a wannan Alhamis.

Hukumar ta ce, sabon daukar nauyin shi ne mafi girma da aka gani a tarihin kwallon kafa a kasar ta Kenya.

A karkashin hadakar, za a rika biyan kowane klub da ke taka leda a gasar lig din ta Kenya akalla Shilling miliyan 8 a kowacce shekara.

Wannan na zuwa ne a bayan kamfanin SportPesa ya janye daga daukar nauyin gasar ta Kenya a cikin watan Satumba sakamakon rikicin kudin haraji tsakaninsa da gwamnatin kasar.

Betking ya tsallaka zuwa Kenya ne a daidai lokacin da gasar firimiyar Najeriya ke fuskantar matsaloli da dama, ciki har da batun daukar nauyi.

WASANNI
KWALLON KA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *