June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Magu ya musanta rahotannin da ke danganta shi da rashawa

1 min read

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya da aka dakatar, Ibrahin Magu ya sake rubuta wata wasika zuwa ga kwamitin bincike karkashin Mai Shari’a Ayo Salami, yana mai musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada dake danganta shi da rashawa yayin da yake a tsare.

TALLA
Magu, ta hannu lauyansa Wahab Shittu, ya kuma zargi kwamitin binciken da kin ba shi isasshen lokaci da damar kare kansa.

A wasikar da ya mika wa kwamitin binciken a ranar Laraba, Magu ya ce kwamitin bai ba shi wasikar da ke kunshe da zarge zargen da ake mai da ke da nasaba da rashawa ba, haka kuma rahoton binciken da aka gudanar a game da kadarorin da hukumar EFCC ta kwato.

Kwamitin bincike karkashin tsohon shugaban kotun daukaka kara ta Najeriya Ayo Salami, na binciken Mr Magu ne kan zargin rashawa da rashin biyayya ga na gaba da shi kamar yadda ministan shari’ar kasar Abubakar Malami ya shigar da koke.

A makon da ya gabata ne dai aka kame Magu don ya amsa tambayoyi, aka kumasallame shi ranar Laraba bayan shafe kwanaki 10 a tsare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *